Aikin fadakar da al'uma kan rajistar zabe a Najeriya
February 16, 2018A kokarin shawo kan koma bayan masu jefa kuri’a da ma bukatar karbar katin zabe a Najeriya, gamayyar kungiyoyin farar hula sun yi maci don wayar da kan jama’a kan alfanu da kuma illolin da ke tattare da hakan a kokari na samun zaben na gari a tsarin mulkin dimokradiyya a Najeriya. Gamayyar matasan sun yi maci ne dai a birnin Abuja domin bayyana muhimmanci fitowa a jefa kuri’a a zabukan da ke tafe a Najeriya. Raguwar adadin masu jefa kuri’a a zabukan Najeriyar duk da sha’awar siyasa da aka san al'umar kasar da ita, musamman ma dai mata da matasa, babban matsala ce da ke kalubalantar daukacin tsarin zabe da ma demokradiyyar kasar. Abin da ya daga hankalin kungiyoyin shi ne jan kafa da jama’a ke yi wajen sabunta rajistarsu ta katin jefa kuri’a a kasar a yanzu. A wasu zabukan gwamnoni da aka yi, abin ya ja baya zuwa kashi 22 cikin 100.
Nuna damuwa a kan raguwar yawan adadin mutane da ke jefa kuri’a a Najeriyar na nuna a fili yadda aka fara kai al'umma bango a kan kaiwa ga samun romon demokradiyya da suka yi koken basu gani a kasa, ko kuwa an zabi shugabannin da ke gallaza masu azaba. Ko mece ce mafita daga wannan matsala ganin Najeriyar na fuskantar wasu zabukan ga kuma aikin sabunta rijistar na fuksntar wannan matsala? Ana dai cike da fatan cewa gangami irin wannan zai ankarar tare da wayar da kan al'ummar Najeriya a kan muhimmancin jefa kuri’a da ma karbar katun kansa a kasar.