1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwangilar gina hanyar Lusaka

Zainab Mohammed Abubakar
April 4, 2023

Zambiya na shirin sake gina hanyar Lusaka zuwa Ndola mai tsawon kilomita 327, a wani aiki da ake sa ran zai lakume sama da dalar Amurka miliyan 577.

https://p.dw.com/p/4PhR0
Sambia | Amtseinführung Präsident Hakainde Hichilema
Hoto: Salim Dawood/AFP/Getty Images

Gwamnatin Zambiya ta sanar da shirin sake gina hanyar Lusaka zuwa Ndola mai tsawon kilomita 327 zuwa wata babbar hanyar da ta rabu, a wani aiki da ake sa ran zai lakume sama da dalar Amurka miliyan 577 kwatankwacin Euro miliyan 528.

Shirin, wanda ya dade yana aiki, tsohon shugaban kasar Edgar Lungu ne ya fara tunaninsa kan dala biliyan 1.2. Lungu ya fuskanci kakkausar suka kan wannan makudan kudade, kuma ya kasa aiwatar da shi saboda karuwar basussukan da ake bin Zambia.

A shekarar da ta gabata ne shugaban kasar na yanzu Hakainde Hichilema ya soke rancen dala biliyan 1.6 daga bankunan kasar Chaina bayan da Zambiya ta kasa biyan basussukan da ake binta daga kasashen waje. Za a ayi amfani da kukaden rance ne wajen aiwatar da aikin hanya.