1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya: Kammala hawan Arfat

Binta Aliyu Zurmi LMJ
July 19, 2021

Mahajjatan bana sun shiga rana ta karshe a gudanar da farillan aikin hajji, a yayin da suka yi hawan Arfa a wannan Litinin din. 

https://p.dw.com/p/3whFc
Haj und Eid Al Adha 2021
Hoto: Ahmed Yosri/REUTERS

Wannan shi ne karo na biyu da mahajjata ke gudanar da aikin a yanayi na corona, sanye da takunkumi da kuma bayar da tazara domin tabbatar da bin matakan kariya daga cutar. A bana ma dai an takaita yawan mahajjatan saboda annobar ta corona, inda maimakon mutane sama da miliyan biyu da ke halarta aikin Hajjin a kowacce shekara, mutan dubu 60 ne kacal mazauna Sauduiyyan wadanda suka yi allurar riga-kafin cutar aka bai wa izinin yin aikin hajjin. Sai dai duk da haka, adaadin ya wuce na shekarar bara, inda mahajjata dubu 10 ne kacal suka ziyarci dakin Allah.