Cika yarjejeniya tsakanin Jamus da Namibiya
March 22, 2023Tun a karshen watan Janairu aka soma gudanar da shari'ar a gaban babbar kotun Namibiya. Alkalai na kokarin neman dakatar da shirin sulhu na Jamus. Madugun 'yan adawa na Namibiya Bernadus Swartbooi da wasu fitattun wakilan Herero da Nama suke neman a yi haka.
Karin Bayani: Jamus na adawa da sabon zama da Namibiya
Sai dai ana ganin idan wadanda suka shigar da kara sun yi haka ne da nufin yin matsin lamba ga gwamnatin Jamus da alama sun makaro saboda gwamnatin Jamus da gwamnatin Namibiya sun amince cewar ta hanyar sulhu ne kawai ake iya warware matsalar tare da cewar dole ne a fayyace wasu tambayoyi a fili ta hanyar sake tattaunawa. Sevim Dagedelen ‚‘yar majalisar dokokin Jamus Bundestag ta jam'iyyar Die Linke ta ce akwai kuskure a ciki.
Mataki da gwammnatin ta Jamus ta dauka dai na yin tattaunawar kawai da gwamnatin Namibiya ba tare da wakilan Herero da Nama ba da kuma sauran al'ummar ya janyo martani cikin fushi a Namibiya. Lifalaza Simataa jigo ne daga jam'iyyar 'yan adawa na Namibiya wanda yake gani babu wani wakilici mutanen Namibiya da ke cikin wannan yarjejeniyar.
Gwamnatin Jamus ta yi tsayin daka kan batun biyan diyya da ake ta cece-kuce da shi wadda ta ba da shawara biyan Yuro (Euro) biliyan 1.1 a tsawon shekaru 30. Kudin dai za a gudanar da aikin raya kasa a yankunan Herero da Nama. Sai wakilan Herero da Naman suna neman a biyasu diyya a hukumance.. Nandiuasora Mazeingo shugaban wata kungiyar da ke saka ido kan kisan kare dangin ya ce ya zama wajibi a biya kudin diyya. Masu adawa da abin da ake kira "yarjejeniyar sulhu" a yanzu suna jiran ganin hukuncin da kotu za ta yanke a Namibiya.