Al-Burhan ya bukaci MDD ta kawo karshen ayyukanta a Sudan
November 18, 2023Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kawo karshen aikin tabbatar da zaman lafiya a kasar da ke fama da yakin basasa. Dama dai Janar Al-Burhan ya dade da zargin Majalisar ta Dinkin Duniya da haddasa rikici a kasar da yake jagoranta, lamarin da ya haddasa tsamin dangantaka tsakanin sassa biyu.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke Khartoum ta aika wa tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan wata wasika, inda ta nemi UNITAMS mai dauke da fiye da ma'aikata 400 galibin su farar hula, da ta dakatar da aikinta nan take . A halin yanzu dai ana ci gaba da gwabza kazamin fada a Sudan tsakanin sojojin da ke karkashin jagorancin shugaban mulkin sojin kasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun sa-kai na mataimakin shugaban kasar Mohammed Hamdan Daglo da aka kora daga bakin aiki.