Bikin bajekolin Al-Kur'anai a Iran
May 14, 2019Wakilai daga cibiyoyin addini da ma'aikatun gwamnati da wakilan majalisun dokoki gami da alarammomi da shehunan maluma da masana daga jami’oi daban-daban na kasashen musulmi ne suka halarci bikin baje kolin da akai wa taken Al-kur'aninmu daya makomarmu ma daya ce. Daga cikin bangarori 700 da aka gabatar ga babban kwamitin tantance ayyukan baje kolin, batutuwa 126 ne aka tantance za ai baje kolin a kansu, ciki har da nuna nau'o'in kwafin Al-Kur'ani da aka rubuta su da hannu kan fararen takaddu da alluna na katako da kuma kan fararen kirtanai. Muhammed Tamim Sahibzadeh masanin zane ɗan ƙasar Afghanistan ya kaddamar da wani Al-Kur'ani mai girma da ya shirya a cikin shekaru biyu da rubutun ruwan zinariya da siliki.
An dai yi amfani da sinadarai da dama domin rubuta wannan Al-Kur'anin mai nauyin sama da kilo takwas da kuma shafuka 610. Tamim Sahibzadeh ya yi amfani da salon rubutu da siffofi irin na Al-Kur'anan karni na 15 da 16. Bugu da kari an gabatar da wasu manhajojin fasahar zamani da zasu taimakawa buga Al-Kura'ani tare da larabin da zai dinga fayyace ayoyi masu kamanni da juna da kididdigar masu kamanni a Al-kur'anin da nufin taimakawa wajen samun saukin hadda. Wakazalika, an baje kolin tsarin ayayoyin Al-Kur'anan da ake ratayensu ko mannawa a gidaje da jikin abababen hawa da ofisoshi da masallatai, kai hatta wadanda ake ratayawa a wuya ko dantse da ke zama yayi ga matasa da 'yan matan kasashe daban-daban.