1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al-Qaida a Pakistan ta musanta hannu a kisan Bhutto

December 29, 2007
https://p.dw.com/p/Chqd

Ɗan takifen nan mai alaƙa da ƙungiyar Al-Qaida a Pakistan Baitullah Mehsud ya musanta cewa yana da hannu a kisan gillan da aka yiwa tsohuwar Firaministan Pakistan Benazir Bhutto. Mehsud ya ba da wannan sanarwa ne bayan da ma´aikatar cikin gidan Pakistan ta zargi sojojin sa kai na al-Qaida da Taliban da hannu a harin ƙunar bakin waken da aka kai a birnin Rawalpindi, wanda yayi sanadiyar mutuwar Misis Bhutto. Da farko ma´aikatar cikin gidan ta ce ta tare wani sako na wani shugaban sojojin sa kai yana taya magoya bayansa murnar samun nasarar kashe Bhutto. Ana fama da zaman ɗar-ɗar a faɗin ƙasar ta Pakistan bayan wannan kisa. Kawo yanzu mutane akalla 32 suka rasa rayukansu a tashe tashen hankulan yin tir da kisan gillan.