Al-Qaida ta kai mumunan hari a ma'aikatar tsaro a Siriya
February 25, 2017Talla
Kungiyar kare hakin bil-Adama ta kasar ta Siriya ce dai ta bada adadi, yayin da gwamnan jihar ta Homs Talal Barazi, ya ba da adadin mutane 30 da suka mutu, da kuma wasu 24 da suka samu raunuka. Wannan hari dai ya kasance mafi muni da aka kai a birnin na Homs a cewar Rami Abdel Rahmane shugaban kungiyar kare hakin bil-Adama ta kasar ta Siriya.Tuni dai tsofuwar kungiyar Al-Qa'ida a kasar ta Siriya ta dauki alhakin kai harin, a daidai lokacin da ake kokarin tattaunawa tsakanin bangaran gwamnatin ta Siriya da 'yan adawa a birnin Jiniva. A hannu daya kuma adadin wadanda suka mutu a harin da Kungiyar IS ta kai a ranar Juma'a kusa da birnin Al-Bab ya kai na mutane 77 cikinsu fararan hulla 41.