1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Al shabaab ta halaka mutane

February 4, 2019

Kungiyar ta'addanci a Somaliya ta kai wani hari da ya yi sanadin salwantar mutane a wannan Litinin.

https://p.dw.com/p/3CgWg
Kenia Angriff auf Hotel in Nairobi
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Rahotannin da ke fitowa daga Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, na cewa kungiyar al Shabaab ta halaka akalla mutum 11 a wani harin bom da ta kaddamar kusa da wata cibiyar hada-hada da ke a birnin.

'Yan sanda sun tabbatar da harin wanda ya shafi wasu cibiyoyin da suka hada da bankuna da shuganan sayar da hajoji.

Harin dai an kai shi cikin wata motar da aka shake ta da boma-bomai, wadda aka tsayar da ita a harabar cibiyar.

Akwai kuma wasu mutum 15 da suka jikkata a lamarin a cewar hukumomin tsaro a Somaliyar.

Al-Shabaab dai na ikirarin jihadin neman kafa gwamnati ne a kasar wacce ta saba wa tsarin kasashen yamma.