Al-Shabaab ta kai hari a Mogadishu
March 23, 2022Talla
Shaidun gani da ido sun ce an yi musanyar wuta a cikin filin saukar jiragen saman a artabun da aka kwashe sao'i ana yi a sa'ilin da wasu mutanen guda biyu dauke da makamai suka kai harin. Akalla an kashe sojin gwamnatin daya yayin da wasu da dama suka jikkata, sai dai kawo yanzu ba a da masaniya kan ko dakarun gwamnatin sun yi nasarar murkushe 'yan ta’addar. A shekara ta 2011 sojojin rundunar kiyaye zaman lafiya na Amison suka kori Al Shebab da ke yakar gwamnati daga Mogadishiu. Sai dai har yanzu tana rike da yankuna da dama na karkara, kana tana ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da na sojoji.