1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum 10 sun mutu a harin Somaliya

Ramatu Garba Baba
November 28, 2022

Mutum akalla 10 aka tabbatar sun mutu a sakamakon harin da mayakan Kungiyar al-Shabab suka kai kan wani hotel da ke kusa da fadar gwamnatin kasar Somaliya.

https://p.dw.com/p/4KADq
Mutum akalla 10 sun mutu a harin SomaliyaHoto: Farah Abdi Warsameh/AP/picture alliance

An yi musayar wuta a tsakanin jami'an 'yan sanda da mayakan na al-Shabab a hare-haren da mayakan suka kai kan wani hotel da ke kusa da fadar gwamnati a Mogadishu babban birnin kasar. Daga cikin wadanda harin na ranar Lahadin da ta gabata ya rutsa da su, har da wasu mutum biyu da ke da asali da Britaniya, a yayin da Ministan harkokin tsaron kasar Ahmed Mohamed Doodishe ya tsira da mummunan rauni.

Kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin a wani sako da ta aika kai tsaye zuwa gidan rediyon gwamnatin kasar a daidai lokacin da ake musayar wuta a tsakaninta da jami'an tsaro a ginin hotel din. Kwanaki biyu da suka gabata, rundunar sojin Somaliyan ta ce, ta yi nasarar hallaka mayakan al-Shabab kimanin dari, ciki har da shugabanin kungiyar akalla goma, lamarin da ya sa ake kallon wannan harin a matsayin na ramuwar gayya.