Al-Shabab za ta ƙyale ƙungiyoyin agaji na duniya kai ɗauki Somaliya
July 6, 2011Sojojin sa kan ƙasar Somaliya masu alaƙa da ƙungiyar Al-Qaida waɗanda suka kori ma'aikatan agajin ƙetare daga yankunan dake ƙarƙashin ikonsu a shekarun baya, yanzu suna kira da a kai ɗauki ga dubban mutane dake fama da masifar fari da kamfar ruwa a Somaliya.
Ƙungiyar ta Al-Shabab ta Musulmi sojojin sa kai dake iko da mafi yawan yankunan Somaliya ta ɗage haramcin da ta ɗora kan hukumomin ba da taimakon abinci na duniya. Hakan ta zo ne a daidai lokacin da ƙasar ta Somaliya ke fuskantar matsalar fari mafi muni cikin shekaru 60. Ƙungiyar ta Al-Shabab wadda ke da alaƙa da Al-Qaida ta yi kira da a taimakwa dubbannen mutane da farin ya shafa. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta nunar da cewa ƙarancin abinci da tashe tashen hankula sun tilastawa 'yan Somaliya su kimanin dubu 50 tserewa daga ƙasar a cikin watan Yuni kaɗai. A cikin shekara ta 2009 Al-Shabab ta sanya haramcin ga taimako daga ƙetare inda ta zargi hukumomin agaji da ƙyamar addinin Musulunci. Yankin ƙahon Afirka dai na fama da mummunan fari wanda ya tilasta dubban mutane dogaro ga taimakon abinci, wanda kuma ya haddasa ƙauran mutane musamman daga Somaliya zuwa Kenya da Ethiopia.
Mawqallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu