Akalla mutane tara sun mutu a kusa da Mogadishu
October 3, 2022Talla
Kwamandan rundunar 'yan sandan kasar Mohamed Moalim Ali ya ce ko baya ga muutane da suka mut, hari ya kuma raunata mutane 10. Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa fashewar motocin biyu da aka kai harin da su ya lalata gidaje da dama. Harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Somaliya ta ambaci kisan wani jigo na kungiyar Al-Shabab, wanda tun daga farko ta bayar da tukuycin makudan kudi ga duk wanda ya kwarmata mata inda yake.