Al-Sisi da Benjamin Netanyahu sun gana
September 19, 2017Talla
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun gana a karon farko abin da Masar ta ce wani bangare ne na kara farfado da shirin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
A cewar mahukuntan na Masar shugabannin biyu sun gana a ranar Litinin a wani bangare na taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, Sisi ya kuma gana da Mahmoud Abbas shugaban Falasdinawa inda suka amince da ci gaba da bibiyar batun kasancewar Isra'ila da yankin Falasdinawa su ci gaba da zama a matsayin kasashe biyu da ke zama da juna cikin mutunci.
Har ila yau wannan zama na zuwa kwanaki bayan da Masar ta shiga tsakanin Fatah da Hamas bangarori biyu na Falasdinu da ke gaba da juna.