1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

al-Sisi ya karbi jagorancin Kungiyar AU

Abdul-raheem Hassan
February 10, 2019

Wa'adin shugabancin Shugaba Paul Kagame na kasar Ruwanda ya kawo karshe a lokacin da Kungiyar Tarayyar Afirka ke fara taronta a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

https://p.dw.com/p/3D6CV
Äthiopien Gipfeltreffen der Afrikanischen Union in Addis Abeba Übergabe AU-Vorsitz
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Shugaba Kagame ya maida hankali ne kan farfado da cibiyoyi da harkokin gudanarwar kungiyar, yayin da ake sa ran sabon shugaban kungiyar al-Sisi ya jajirce kan batun tsaro da wanzar da zaman lafiya.

Sakatare janar na Majalisar DInkin Duniya Antonio Guterres ya jinjinawa nahiyar Afirka tare da bayyana kyakkyawar fata kan nahiyar nan gaba musamman kan yadda aka gudanar da zabuka a kasashen Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Mali da Madagaska da ma yarjejeniyar zaman lafiya a Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da farfado da huldar diplomasiyya tsakanin Habasha da Iritiriya.