1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A-Sisi ya sake lashe zaben shugaban kasa

Zainab Mohammed Abubakar
March 29, 2018

Kwarya kwaryar sakamakon zaben shugaban kasa a Masar na nuni da cewa, an sake zabar Abdel Fattah al-Sisi, a karo na biyu da kashi 92 daga cikin 100 na yawan kuri'u da aka kada.

https://p.dw.com/p/2vCVT
Griechenland Ägyptischer Präsident Al-Sisi
Hoto: Reuters/Y. Kourtoglou

Mutane miliyan 23 daga cikin miliyan 60 da suka yi rijistan yin zabe ne dai suka kada kuri'insu, a zaben na kwanaki uku da aka kammala a jiya Laraba, a cewar kamfanin dillancin labarun masar watau MENA.

Babban mai kalubalantar Sisi Moussa Mostafa Moussa dai ba wani sanannen mutum ba ne a kasar, kuma shi  ma mai goyon bayan shugaba Sisi ne, mutumin da ya yi rijistar yin takara kwanaki kalilan gabannin zaben, a wani mataki na kaucewa takarar mutun daya.

Sisi da ke zama hafsan soji, ya kifar da gwamnatin zababben shugaban kasar ta Masar na farko Mohamed Morsi, bayan gagarumin gangamin adawa a shekarata 2013, inda daga bisani ya lashe zaben wa'adinsa na farko a shekarata 2014.