1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan sabon shugaban kungiyar AU

Mahmud Yaya Azare RGB
February 11, 2019

Zaben shugaban Masar, Abdelfattah al-Sisi a matsayin shugaban Tarayyar Afirka ya janyo martani mabanbanta daga bangarori daban-daban.

https://p.dw.com/p/3D8BV
Äthiopien Gipfeltreffen der Afrikanischen Union in Addis Abeba Übergabe AU-Vorsitz
Hoto: Reuters/T. Negeri

Zaben na Shugaba Abdelfattah al-Sisi na Masar dai, ya zo ne mako guda bayan da aka rataye wasu matasa uku 'yan adawa a kasar bisa zargin su da hannu wajen kashe wani dan alkali, a shari'ar da masu fafutuka suka ce tsagwaron sharri ne. Tuni ma dai kungiyoyi kare hakkin dan Adam irin su Amnesty International suka siffanta nadin nasa da wani mummunan koma baya a nahiyar Afirka.

A hannu guda, wasu da ke jinjinawa wannan matakin sun ce ya kamata Afirka ta daina mafarki ta dinga fuskantar abun da ke aukuwa a kasa, domin shi kansa Shugaba al-Sisi zaben shi a ka yi kuma a daidai lokacin da shugabannin kasashen na Afirka ke fama da matsalolin tsaro da na ta'addanci, ganin cewa shi shugaban na Masar cikin karamin lokaci ya gama da wannan annoba a Masar, hakan ta sanya ya cancanci a danka masa wannan ragama, musamman bayan da akai ta jinsa yana tayin tallafawa shuwagabanin nahiyar magance wannan annoba.

Tun bayan da shugaban na Masar ya dare kan karagar mulkin kasar, ya ke ta zawarcin shuwagabannin Afirka da kokarin ganin ya dasa da su, a yunkurinsa na dawo da tsohuwar alaka ta kut da kut da ake da ita tsakanin Masar da kasashen na Afirka tun zamanin Shugaba  Gamal Abdel Nasser wacce shugabannin na Masar da suka zodaga baya su ka gagara rike ta, lamarin da ya bai wa babbar abokiyar hamayyarta a yankin Isra'ila damar yin kaka gida a Nahiyar.