1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Alamar ta'addanci a harin birnin Paris

Gazali Abdou Tasawa
October 5, 2019

Hukumomin shari'a a Faransa sun maida aikin bincike kan harin da aka kai wa 'yan sanda a Paris a hannun hukumar yaki da ta'addanci bayan da bincike ya gano alamar alaka da tsattsauran kishin Islama ga maharin.

https://p.dw.com/p/3QlW3
Paris nach Messerattacke
Hoto: AFP/G. van der Hasselt

Faransa ta sanar da maida bincike kan kisan 'yan sanda hudu da wani jami'in babbar hukumar 'yan sandan birnin Paris a ranar Alhamis da ta gabata a hannun hukumar yaki da ta'addanci ta kasar bayan da aka samu wasu karin bayanai a kan mutumin da ya kai harin da ke nuni da cewa matakin harin nasa ba ya rasa nasaba da ta'addanci irin na masu tsauttsauran ra'ayin Islama.

Sakamakon binciken da aka yi ya zuwa yanzu ya gano cewa mutumin mai suna Mickael H dan shekaru 45 ya karbi Muslunci yau da shekara daya da rabi a hannu wasu Salafawa. Kuma binciken ya gano cewa ya tsara harin nasa ne kafin ya kai shi.

A ranar Alhamis da ta gabata ce dai mutumin wanda jami'i ne a babbar hukumar 'yan sanda ta birnin Paris, ya kai hari da wuka kan 'yan sanda a babbar hedikwatarsu da ke a birnin Paris, inda ya halaka hudu daga cikinsu kafin wani dan sandan ya bindige shi.