1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

240811 Nahost Gewalt

August 24, 2011

Bayan wasu hare-haren da aka kai a yankin shaƙatawa na Eilat dake iyakar Isra'ila da hamadar Sinai, sojojin Isra'ilar sun mayar da martani ta kai farmaki kan wasu yankuna a zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/12NC4
Hoto: AP

To sai dai kuma a halin da ake ciki yanzu an cimma daidaituwa akan tsagaita wuta tsakanin ƙungiyoyin Palasɗinawa da mahukuntan Isra'ila. Amma ayar tambayar dake akwai ita ce, shin wane ne ke da alhakin hare-haren akan kudancin Isra'ila? A can zirin Gaza dai babu wata ƙungiyar da ta fito ta ɗauki alhakin lamarin.

A dai yankin iyaka na Erez tsakanin Isra'ila da Gaza, babu wata alamar dake yin nuni da tsagaita wuta. Sojojin Isra'ila da aka tsugunar a wata hasumiyar tsaro akan iyakar Isra'ilar da Gaza su kan buɗe wuta akan Palasɗinawan da suka yi kurarin kusantar iyakar.

Dangane da garin Gaza kansa kuwa al'amuran rayuwa na tafiya kamar yadda aka saba yau da kullum, babu wata alamar dake nuna fuskantar hargitsi da Isra'ila a baya-bayan nan da mayar da martanin Isra'ila tare da harin da sojan Isra'ila suka kai kan jami'tsaron iyakar ƙasar Masar. Dangane da harin da aka kai kan farar hula a kudancin Isra'ila ba wanda ya yarda ya ɗauki alhakin harin a zirin Gaza. Mustafa Sawaf, ɗan jarida na kurkusa da ƙungiyar Hamas, ya yaba da harin:

"Wannan mani tsayayyen mataki ne na soja da aka shirya a cikin basira aka kuma wanzar da shi daidai yadda ya kamata. A rikici tsakaninmu da Isra'ila, maganar ta danganta ne da cikakkiyar masaniya akan leƙen asiri da kaifin hankali. Rikici ne na basira. Isra'ila zata daɗe tana tunawa da wannan mataki."

Akasarin waɗanda aka tattauna da su a zirin Gaza dake da dangantaka ta kurkusa da ƙungiyar Hamas suna ɗora wa Isra'ila laifin rikicin na baya-bayan nan. Misali Ahmad Yusuf, babban mai ba wa ƙungiyar Hamas shawara, ya musunta cewar Palasɗinawa daga Zirin Gaza sun buɗe wuta kan motoci da bas-bas a kudancin Isra'ila:

"Bajamushe ma yana iya tasowa daga Jamus zuwa Alƙahira, sannan ya zarce zuwa Sina'i domin isa Eilat. Mai yiwuwa ne ma masu alhakin harin sun fito ne daga Isra'ilar kanta. Kuma ganin cewar har yau ba wanda ya fito fili ya ɗauki alhakin harin, me ya sa ne lalle sai an ɗora mana wannan alhaki? Alhali ma dai ita kanta Isra'ila babu wata shaidar da ta bayar dake tabbatar da cewar masu kai harin sun fito ne daga Gaza."

Hatta a shelkwatar ƙungiyar Jihadil-Islam ba wanda ya haƙiƙance da lamarin. Kakakin ƙungiyar akan manufofin siyasa, Ahmad el-Modallal ya ce ba ya da wata masaniya game da kowane ne ke da alhakin lamarin. Amma kuma ya tafa wa masu alhakin harin:

"Muna ba da goyan baya ga duk wani mataki na adawa da Isra'ila. Wai me Isra'ila ke tsammani ne daga gare mu? Cewar zamu daga fararen tutoci ne? Ba zata iya sa ran ganin haka daga gare mu ba, kuma ba zamu yi hakan ba. A saboda shi muna madalla da duk wani mataki na adawa."

Ƙungiyar ta Jihadin Islama da ita kanta Hamas ba zasu yi kurarin rungumar alhakin harin ba saboda kwadayinsu na mulki, a maimakon haka sun fi sha'awar ganin wani dabam ya fito ya ɗauki wannan alhaki, kamar yadda wata da ake kira Nejwa Dora daga garin Gaza ta nunar:

"Wannan babban kuskure ne. Muna bukatar zaman lafiya, muna buƙatar kwanciyar hankali. Kuma muna buƙatar ganin yaranmu sun taso ƙarƙashin wani yanayi na zaman lafiya."

Mawallafa: Sebastian Engelbrecht / Ahmad Tijani Lawal
Edita: Mohammad Nasiru Awal