Nijar: PNDS na zawarcin zawarcin Albade a zaben 2020 da 2021
August 12, 2020Bayan kai ruwa rana na tsawon wani lokaci, wasu jam'iyun siyasa masu kawance da PNDS Tarayya mai mulki sun yanke shawarar tsayar 'yan takararsu a zaben shugaban kasa mai zuwa, jam'iyyar baya-bayan nan ita ce MPN Jamhuriya ta Albade Abouba wanda shekaru biyar da suka gabata ya yi mubaya'a ga dan takarar jam'iyyar PNDS Tarayya tun a zagayen farko na zaben shugaban kasa, abin da ya fusata wasu magoya bayan jam'iyyarsa da dama.
Matakin da jam'iyyar MPN Jamhuriya ta dauka na a matsayin manuniya ce ga sauran jam'iyyun siyasar kasar da suka jima suna nuna goyoyn baya ga jam'iyyar da ke mulkin kasa, kana matakin ya zo ne bayan da jam'iyyar ta gudanar da babban taronta na kasa inda ta yanke hukuncin tsayar da dan takara sabanin yadda ta yi a shekarun da suka gabata.
Pnds Tarayya ta jima tana zawarcin jam'iyyar MPR ta Albade Abouba a gabanin ya bayyana anniyarsa ta cewa zai tsaya takara, kana ko baya ga jam'iyyun da ke bangaren masu mulki 'yan adawa na ci gaba da fatan ganin jam'iyyar ta sake hadewa da su wajen kulla kawancen da zai basu damar kawar da mulkin jam'iyyar Pnds Tarayya da suka jima suna kalubalanta.
Nan da 'yan watanni kalilan ne za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da zaben mashawartan kanan hukumomi a Nijar, wanda ke a zama zaben farko da jam'iyya mai mulki zata shirya domin mika mulki a hannun wata gwamnatin farar hula da talakawa suka zaba.