1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakin ba-zata na Bouteflika ya janyo murna

Mahmud Yaya Azare
March 12, 2019

Al'ummar Aljeriya na cigaba da yin martani dangane da lashe aman da shugaban kasar ya yi na janye takara a karo na biyar, tare da sanar da dage zaben shugaban kasar

https://p.dw.com/p/3ErCy
Algerien Proteste in Algier
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

Yadda 'yan kasar suka fantsama kan tituna don nuna murnarsu da matakin ba zatan da shugaban Bouteflika ya dauka kna janye takarar tasa ke nan.

 "Da ma muradinmu shine mu tilastamar dakatar da takararsa, kuma Alhamdulillahi munt i nasara. so mu tilastamar janyewaKuma munyi nasara.Ya kyautawa kansa. Ya kuma kyauta kasar Aljeriya.Yanzu dama ta samu da za a tsayar mana da wanda ke da koshin lafiya, wanda kuma zamu fahimci juna."

To sai dai batun dage zaben da aka tsara gudanar da shi a ranar a ranar 18 ga watan gobe,  har sai bayan babban taron da  ya ce zai sake fasalin siyasar kasar, ya sanya wasu na ganin cewa anyi nadi da lauje:

"Ba muga dalilin da zai ce a daage zabe ba.Tunda shi ya janye, ya bar hukumar zabe ta gudanar da aikinta.Mu yan kasa mne da hakkin yin kira a dage zabe ko a gudanar da shi."

Algerien | Abdelaziz Bouteflika
Shugaba Abdelaziz BouteflikHoto: imago/photothek/T. Trutschel

Wala Allah hakanne ya sanya wasu ke ganin matakin na Bouteflika, tamkar an kashe maciji ne ba a yanke kansa ba:

"Wannan matakin farko ne kawai. Har yanzu da sauran rina a kaba. Bukatar al'ummar aljeriya ita ce, samar da sauyi na hakika, da kifar da gungun  azzuliman da ke cutar da kasa.”

Wata baiwar Allah da ta ce da ita akai tayin  zanga-zangar makwanni ukun da suka gabata, ta bai wa shugaban shawara kamar haka:

"Boutifilika ba mai wuyar sha,ani bane,wadanda ke kewaye dashi ne mugaye, suke rawa da bazarsa.Don haka muke kira garesu da suji tsoron Allah su bar al'ummar Aljeriya su zabawa kansu makoma."