Shuga Bouteflika ya bayyana matakin kauracewa shiga takara
March 11, 2019Shugaban Aljeriya da ya gana da shugaban hafsan sojan kasar baqyan ya isa gida a ranar Lahadi 10.03.2019 inda bayyana shirya wani taron da zai kai ga duba hanyoyin kawo gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar domin samar da wani sabon kundin tsarin mulki a wannan shekara. Kana shugaban ya ce ba zai tsaya takarar shugabancin kasa ba yana mai cewa ba ya bukatar wani wa'adi na biyar na mulki duba da yanayin shekaru da kuma rashin lafiya.
Sai dai shugaban ya ce za a dage zaben kasar na shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 18 ga watan gobe har izuwa gabanin babban taron da zai tattara daukacin bangarorin tafiyar siyasar kasar.
Birnin Algers da sauran yankunan kasar sun barke da sowa da hayaniyar motoci bisa jin matakin na Shugaba Abdelaziz Bouteflika wanda ke cika shekarunsa na 20 kenan a kan madafan iko kuma ke fuskantar matsin lanba daga yan kasar da ke cewar ko kadan ba za su lamunta shugaban ya sake tsaywa takara ba saboda rashin lafiya.