Hukuncin shekaru biyu gida yari ga mai fafatuka
March 23, 2020Talla
Lauyan da ke kare matashin ya bayyana shafinsa na Facebook a yau Litinin da cewa alkali mai shigar da kara ya yanke hukuncin zaman gidan waklafin ne na shekaru biyu a yayin wani zama a asirce da kotun ta gudanar a birnin Algers, sai dai lauyan ya ce za a yi gundarin zaman shari'ar ne a ranar shida ga watan gobe.
Wannan hukuncin kotun na zuwa ne a daidai lokacin da ma'aikatar shari'ar kasar ta bayyana dage sauraren duk wata kara a cikin kotunan kasar har ya zuwa 31 ga wanann watan da muke ciki.