1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin kasashen Aljeriya da Maroko

Mahmud Yaya Azare LMJ
September 23, 2021

Makonni uku bayan katse huldar diplomasiyya da Maroko, Aljeriya ta rufe iyakokinta na sararin samaniya da kasar, lamarin da ya jefa al'umomin kasashen biyu cikin halin tsaka mai wuya.

https://p.dw.com/p/40ksM
Flaggen | Algerien und Marokko | Symbolbild
Dangantaka tsakanin Aljeriya da Maroko ta tarwatseHoto: daniel0Z/Zoonar/picture alliance

Majalisar kolin tsaron kasar ta Aljeriya ce dai, bayan wani taronta na gaggawa ta sanar da matakin rufe iyakokin sarararin samaniyarta da makwabciyar tata Maroko. Aljeriyan dai ta kai ga daukar wannan matakin ne, kan abun da ta kira ci gaba da daukar matakan zagon kasa da neman tsokalar fada da Marokon ke mata. Ministan harkokin wajen kasar ta Aljeriya Ramtane Lamamra dai, ya yi karin haske kan wannan batu: "Aljeriya ba za ta lamunci wasu take-taken zagon kasa da Maroko ke yi a iyakar kasarmu ba, wadanda ba kasar Aljeriya kadai za su jefa cikin bala'i b, har ma da dukkanin al'ummomin yankin yammacin Sahara."

Algerien bricht die Beziehungen zu Marokko ab
Ministan harkokin wajen Aljeriya Ramtane Lamamra yayin jawabinsa kan MarokoHoto: Hamza Zait/AA/picture alliance

Tsohon rikici tsakanin kasashen biyu dai, ya samo asali daga sabanin kan iyakoki bayan da suka samu 'yancin daga kasar Faransa, da kuma goyan bayan kungiyoyin 'yan aware tsakaninsu. A nata bangaren, ma'aikatar harkokin wajen Maroko, ta nuna takaicinta da wannan matakin da Ajeriyan ta dauka wanda ta ce ya sabawa dokokin kasa da kasa. Ta kara da cewa, zarge-zargen da Aljeriya ke mata ba su da tushe balle makama. Yunkurin da kasashen Saudiyya da Kuwait da ma kungiyar kasashen Larabawa suka yi ta yi a makonni biyun da suka gabata domin sasanta kasashen biyu dai, za a iya cewa yabi ruwa. Wannan lamari dai ya sanya al'umomin kasashen biyu nuna takaicinsu da matakin da suka tabbatar su zai fi shafa.