Faransa za ta biya iyalan sojojin Aljeriya diyya
February 21, 2022An fitar da sanarwa a yayin tuni da ranar kawo karshen yakin neman 'yancin kan kasar Aljeriya. Majalisar Dokokin Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka, ta amince da wani kudiri da zai nemi gafarar 'yan kasar da suka yi wa Faransan yaki tare da biyansu diyya, kudirin dokar ya tanadi biyan diyyar tsakanin yuro dubu biyu zuwa dubu goma sha biyar ga iyalan sojoji da aka kiyasta sun kai dubu hamsin, an ware kimanin yuro dari uku da goma da za a biya a cikin shekaru shidda.
Baya ga wannan, Faransa ta kara nuna alhini kan abin da ya gudana a wancan lokacin, inda ta ce, babu wani lafazi da duk taushinsa, da zai kauda radadin ta'asar da aka tafka, sai dai abin farin cikin, shi ne, yadda aka kama hanyar sasantawa a tsakanin kasashen biyu.
Shekaru sittin kenan da Aljeriya ta sami 'yancin kanta daga Faransa, rikicin kwatar 'yancin kai da wasu da suka biyo baya a tsakaninsu, sun janyo asarar rayuka kimanin miliyan daya da rabi duk da cewa mahukuntan Paris sun baiyana shakku kan wadannan alkaluman.