1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta fara mayar da 'yan Nijar gida

Ahmed SalisuDecember 8, 2014

Mahukuntan Aljeriya sun ce sun fara iza keyar dubban 'yan Nijar da ke zaune a kasar ba bisa ka'ida ba kana suke yin aiyyuka ba tare da bin ka'idojin da gwamnati ta gindaya ba.

https://p.dw.com/p/1E123
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Wata jami'ar humumar bada agaji ta Algerian Red Crescent Sa'ida Ben Habyles ta ce ya zuwa yanzu an tattara 'yan Nijar din kimanin 318 kuma suna birnin Tamanrasset da ke kudancin kasar inda daga nan ne za a kaisu Agadez da ke arewacin Nijar. Galibin mutanen dai mata ne da kananan yara.

A watan da ya gabata dai Firaminsitan Nijar din Brigi Rafini ya bukaci 'yan kasar da su guji ficewa daga cikinta don zuwa makota neman abin duniya saboda irin hadarin da suke fadawa, yayin da mahukuntan Aljeriya suka nemi kasashen duniya da su agaza Nijar din wajen samawa mutanenta abin yi wanda zai hana su barin gida.