1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya ta sa zare da Maroko

Abdul-raheem Hassan
September 23, 2021

Dangantakar Aljeriya da Maroko ya dauki sabon salo, bayan da gwamnatin Aljeriyar ta killace sararin samaniyarta don hana jiragen saman Rabat shiga iyakarta ta sama.

https://p.dw.com/p/40gl0
Flaggen | Algerien und Marokko | Symbolbild
Hoto: daniel0Z/Zoonar/picture alliance

Fadar shugaban kasar Aljeriya ta ce kwamitin tsaro na kasar, ya cimma wanna matsaya ne ganin yadda ake ci gaba da tunzura jama'a da kiyayya daga bangaren Marooko. Sai dai gwamnatin Maroko ba ta mayar da martani kan wannan zargi ba tukuna.

Rikici ya barke ne tsakanin kasashen Laraban guda biyu da ke arewacin Afirka, tun bayan da Amirka ta goyi bayan Maroko na mallakar yankin Sahara a wani abin da ake ganin sakayya ce na sake kulla kawance da Isra'ila, yayin da Aljeriya ke zargin Rabat da taimaka wa kungiyar aware da ake tuhuma da haddasa gobarar dajin da ya kashe mutane 65.