Aljeriya ta nuna damuwa kan soke yarjejeniyar sulhu a Mali
January 26, 2024Tun a shekara ta 2012 ne dai ake gwabza fada tsakanin mayakan tawaye da na 'yan awaren kasar Mali, kuma Aljeriya ce babbar mai shiga tsakani a yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati, da galibin kungiyoyin Abzinawa masu dauke da makamai suka rattabawa hannu a birnin Algiers.
Sai dai a jiya alhamis ne mahukuntan mulkin sojan kasar ta Sahel, suka ayyana kawo karshen yarjejeniyar da ake ganin tana da matukar muhimmanci ga tabbatar da zaman lafiya a Mali, bayan shafe watanni ana gwabza fada.
Hakan na zuwa ne a yayin da dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD ke janyewa daga arewacin kasar mai fama da rikici.
Gwamnati a Bamako ta zargi "canji halin wasu kungiyoyin" da kuma zargin Aljeriyar da karbar bakuncin wasu wakilan kungiyoyin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da a yanzu suka zama manyan 'yan ta'adda".