1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Aljeriya: An zabi shugaban kasa na riko

Yusuf Bala Nayaya
April 9, 2019

Abdelkader Bensalah da aka zaba ya yi rikon mulkin kasar ba shi da dama ta shiga takarar zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya nunar.

https://p.dw.com/p/3GVp8
Abdelkader Bensalah
Hoto: AFP/P. Kovarik

Majalisar dokokin Aljeriya ta bayyana Abdelkader Bensalah a matsayin shugaban kasa na riko bayan da Shugaba Abdelaziz Bouteflika da ya dauki lokaci mai tsawo yana mulkin kasar ya yi murabus.

Bouteflika ya sauka daga kujerar mulkin Aljeriya a makon da ya gabata bayan wata zanga-zanga mai zafi kan mulkinsa na tsawon shekaru 20 da ta tilasta shugaban ya ajiye mukamin nasa. Bensalah dan shekaru 76 zai jagoranci kasar tsawon kwanaki 90 kafin sabon shugaban kasa bayan zabe. Kuma Bensalah ba shi da dama ta shiga takarar zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya nunar.