Miliyoyi za su shiga macin adawa da Shugaba Bouteflika
March 8, 2019Albarkacin wannan gangamin, an dakatar da duk wata zirga-zirga na layin dogo a duk fadin Algiers babban birnin kasar. 'Yan adawa sun yi wa gangamin lakabi da macin mutum miliyan ashirin. Sun kuma ce zai kasance irinsa na farko a tarihin kasar.
Shugaban mai shekaru tamanin da biyu da haihuwa, ya kwashi fiye da shekaru ashirin ya na mulki amman jama'a sun soma baiyana rashin gamsuwarsu bayan da ya shafe shekaru yana fama da rashin lafiya wanda a dalilin hakan baya ma iya fitowa bainar jama'a. Sai dai a wata sanarwa da Shugaban ya fitar a jiya Alhamis, ya gargadi masu zanga-zangar da su gujewa duk wani lamari da ka iya jefa kasa cikin rudani.
Tun shekarar 2013 rabon da Shugaba Bouteflika ya yi wa jama'rsa bayani kai tsaye.a gabanin gagarumin gangamin da jama'a suka shirya don hana Shugaba Abdel-aziz Bouteflika sake tsayawa takara a zaben kasar mai zuwa.