SiyasaJamus
Adadin sojan Burkina Faso da suka mutu sun karu
November 15, 2021Talla
Adadin sojojin da suka gamu da ajalinsu a wani harin ta'addanci a Burkina Faso sun haura zuwa 32. Tun daga farko dai hukumomin kasar ta Burkina Faso sun bayyana cewa harin da aka kai kan dakarun tsaro na soja da na 'yan sanda a yankin Souma da ke arewacin kasar iyaka da Mali sun kai 20.
Yau tsawon shekaru kenan da kasar da yankin yammacin Afirka mai makwaftaka da Mali da Jamhuriyar Nijar ke fuskantar hare-haren 'yan ta'adda wanda kuma suka yi sanadiyar salwantar rayukan mutane da dama.