1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Allah ya yi wa Helmut Schmidt rasuwa

Arne Lichtenberg/UANovember 10, 2015

Tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Schmidt ya rasu a wannan Talatar bayan ya sha fama da ciwo. Schmidt ya rasu ya na da shekaru 96 da haihuwa.

https://p.dw.com/p/1H3WV
Deutschland Helmut Schmidt Alt-Bundeskanzler schwarz/weiß
Hoto: Getty Images/Cover/P. Junquera

An Helmut Schimdt ne haifeshi ne ranar 23 ga watan Disamba na shekara ta 1918. Da zarar an ambaci Schmidt, Jamusawa da yawa kan tuna shi ne a matsayin mutumin da ya kalubalanci aiyukan tarzoma na 'yan kungiyar RAF a shekara ta 1977, abin da ya sami asalinsa daga sace shugaban kungiyar masu daukar ma'aikatan Jamus Hans Martin Schleyer da kuma fashin jirgin saman kamfanin Lufthansa zuwa Somaliya. An dai yi fashin jirgin ne don yin matsain lamba kan a saki 'yan kungiyar ta RAF da ke tsare a gidajen kurkukun Jamus.

Deutschland Altkanzler Helmut Schmidt auf Intensivstation
Yakin da Schmidt da 'yan tarzoma na daga cikin abubuwan da za a su sa a rika tunawa da shi.Hoto: picture alliance/dpa/C. Charisius

Wannan abin da ya faru shi ne kololuwar al'amuransa na siyasa da ya faro tun misalin shekara guda bayan kare yakin duniya na biyu, lokacin da ya shiga jam'iyar SPD. Tun a lokacin da ya rike mukamin ministan cikin gida a jiharsa ta Hamburg, Helmut Schmidt ya nuna alamun cewar ya kware a fannin iya shawo kan matsaloli idan suka taso. Nan da na kuma likkafa ta yi gaba inda a shekara ta 1964, ya zama shugaban 'yan jam'iyar SPD a majalisar dokokin tarayya. Bayan kafa gwamnatin hadin gwiwa ta SPD da FDP shugaban gwamnatin wancan zamani, Willy Brandt ya maida shi ministan tsaro a shekara ta 1969.

Lokacin da ya zama tilas ga Willy Brandt ya yi murabus, sakamaakon abin kunyar dan leken asirin Jamus ta gabas, Gunther Guillaune, Helmut Schmidt ya zama wanda ya fi dacewa ya gaje shi. To amma duk da wannan sabon matsayi an ci gaba da samun 'yan matsaloli da rashin fahimta tsakanin Schmidt da jam'iyarsa ta SPD saboda matsakaicin ra'ayin da ya ke da shi batun da ya sanya jefi-jefi yakan yi watsi da manufofin da jam'iyar ta tsara ko ta shimfida.

Wannan rashin fahimta ya fito fili a karshen shekarun 1970 dangane da aiwatar da kudirin nan mai fuskoki biyu da kungiyar tsaron NATO ta gabatar. Helmut Schmidt ya bayyana cikakken goyon bayansa game da jibge karin rokokin nukiliyar Amirka a nan Jamus, inda ya kwatanta adawar da jam'iyar sa ta nuna da zanga-zangar da aka rika yi a matsayin al'amura na marasa hangen nesa.

Verleihung des Preises der Atlantik-Brücke an Helmut Schmid
Helmut Scmidt ya yi farin jini sosai a fagen siyasar Jamus.Hoto: Reuters

Jam'iyar SPD ta canza ra'ayinta bayan da Helmut Schmidt ya sauka daga mukamin shugaban gwamnati a shekara ta 1982. Dalilin hakan kuwa shi ne canza sheka da jam'iyar FDP ta yi daga abokiyar hadin gwiwarta a gwamnatin tarayya zuwa jam'iyar adawa ta CDU-CSU. Wannan canji inji FDP na neman canza manufofin kasar a fannnonin tattalin arziki da rayuwar zaman jama'a ne. Schmidt ya ce ko kadan ba zai yarda da yin hakan ba.

A shekarun da suka biyo baya, Schmidt ya janye daga al'amuran siyasa, inda ya zama daya daga cikin mawallafan mujallar mako mai suna Die Zeit. Duk da jawabai na sukan manufofin kungiyar hadin kan Turai da shisshigin Jamus a Afghanistan, amma Schmidt ya ci gaba da kasancewa mai kwarjini da kima a idanun jama'a. A wani ra'ayi na jama'a da aka dauka a shekara ta 2005 an gano cewar Schmidt shi ne mafi farin jini daga cikin dukkanin yan siyasa a tarihin Jamus na baya-bayan nan.