1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Allurar Polio ta sa tsagaita wuta a Gaza

Mahmud Yaya Azare
August 30, 2024

Isra'ila ta da Hamas sun amince da tsagaita wuta na kwanaki uku a Gaza don bai wa hukumar lafiya ta duniya WHO damar gudanar da allurar Polio da ke kara yaduwa a yankin.

https://p.dw.com/p/4k7SC
Gazastreifen El-Zawaida | Polio-Impfungen in Gaza
Hoto: Omar Ashtawy/APA Images/Zumapress/picture alliance

Babban iami'in hukumar lafiyar ta duniya a yankin Falasdinawa, Rik Peeperkorn ya ce suna fatan hakan zai ba da damar yi wa yara kanana kimanin 600,000 allurar ta shan inna a fadin zirin Gaza duk da karancin kwanakin da aka ware don yin ragakafin:

"Babu wanda ke da hanyar samun ishashhiyar damar yi wa wadannan dubban yaran rigakafi cikin tsukin kwanaki uku, sakamakon ragargaza kayayyakin aiki da jin dadin rayuwar jama'a da aka yi a yankin na Gaza. Amma da babu gwara ba dadi. Za mu fara wannan rigakafin mu ga iya abun da zamu iya yi. Fatanmu shi ne a samar da dawwammamiyar tsagaita wuta don lamura su gudana yadda ya kamata a zirin.”

Rikicin Gabas ta Tsakiya - Al-Zawaida
Rikicin Gabas ta Tsakiya - Al-ZawaidaHoto: Naaman Omar/APA Images via ZUMA Press Wire/dpa/picture alliance

Ranar lahadi ce dai ake sa ran za'a fara rigakafin, kuma kamar yadda Kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ke fadi a shirye rundunar sojin ta ke don mutunta wannan yarjejeniyar da za ta ceci rayukan yara kanana ba a yankin Gaza kadai ba harma da yankin Gabas Ta Tsakiya baki daya:

"Kamar yadda a baya muka tsara shigar da kayyakin agajin da suka magance matsalar tsundumar yankin cikin matsananciyar yunwa gami da samar da magunguna a asibitoci da makamashin kunna wutar lantarki da ruwan sha. Rundunar sojinmu za ta tabbatar da dakatar da yaki na tsawan wadannan kwanakin uku. Muna kuma tuntubar shuwagabaninmu na siyasa don duba yiwuwar kara wadannan kwanakin idan ta kama.”

Yaduwar cutar Polio a zirin Gaza
Yaduwar cutar Polio a zirin GazaHoto: Ramadan Abed/REUTERS

 A nata bangaren kungiyar Hamas a ta bakin jami'inta  Basem Naim ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa ƙungiyar a shirye ta ke ta ba da haɗin kai ga kungiyoyin ƙasa-da-ƙasa.

 A farkon watan Agusta ne hukumar lafiya ta Falasdinawa da ke Ramallah ta sanar da bullar cutar ta shan inna da duniya ke ikirarin nasarar kawar da ita daga doron kasa, a zirin Gaza da yawan shara da gawawwakin da ke danne karkashin buraguzai, ya sanya bazuwar cututtuka da annoba ke da saurin yaduwa.

Yaduwar cutar Polio a zirin Gaza
Yaduwar cutar Polio a zirin GazaHoto: Jehad Alshrafi/AP/picture alliance

Abdurrahman dan watanni 10 da aka haife shi cikin rugugin yakin na Gaza, shi ne wanda aka fara gano ya harbu da cutar ta Polio kuma kamar yadda mahaifiyarsa ke roko, ta na fatan tsagaita wutar zai zama sanadin warkewar danta da hana yaduwar cutar zuwa wasu dubban yaran.

“Da koshin lafiyarsa a lokacin da yaki ya tilasta mana kaura zuwa Dair Balah. Haka kwatsam sai kawai jikinsa ya dinga yin zafi da amai, ya daina rarrafe da kiriniyar da ya saba yi. Likitoci suka fada mana cewa ya kamu da shan inna ne, wacce kuma a yanzu babu maganinta ko riga-kafinta a nan. Ina fata in ga dana yia dawo yana tsalle-tsallensa kamar yadda yake ada.”