Al'umar Kamaru na zaben shugaban kasa
October 8, 2018Talla
A wannan Lahadi al'umar kasar Kamaru ke zaben shugaban kasa, zaben da Shugaba mai ci Paul Biya ke neman ci gaba da jagoranci karo na bakwai. Manyan jam'iyyun MRC da FDP masu adawa sun kai ga hadewa daf da zaben, don ganin yadda za su karbe mulki daga hannun Shugaba Biya mai shekaru 85 a duniya. Kasar ta Kamaru na fama da rikice-rikice, musamman a yankinta da ke amfani da turancin Ingilishi, inda alkaluma ke cewa an rasa akalla rayukan fararen hula 420 da sojoji 175 yayin da su kuwa 'yan aware, bila adadin.
Ko a Juma'ar da ta gabata ma dai, an kashe wasu 'yan aware uku a birnin Buea da ke yankin kudu maso yammacin kasar, yankin da masu gwagwarmayar ballewa ke ikirarin sai sun kafa kasa.