1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Zabe da matsi na tattalin arziki

Abdourahamane Hassane
June 18, 2021

Al'umma na kada kuri'a a Iran domin zaben sabon shugaban kasa da zai gaji  Hassan Rohani, mutane kusan miliyan sitin ne wadanda aka yi rijista za su kada kuri'a.

https://p.dw.com/p/3v8xG
 Ebrahim Raisi dan takarar da ake tsamani zai samu nasara a zaben
Ebrahim Raisi dan takarar da ake tsamani zai samu nasara a zabenHoto: Ebrahim Noroozi/AP Photo/picture alliance

'Yan takara hudu ne ke faffatawa a zaben bayan da uku suka janye wanda ake hasashen Ebrahim Raisi mai matsagaicin ra'ayi zai samu nasara. Jagoran addini  Ayatollah Ali Khamenei ya yi kira ga jama'ar kasar da su fito don kada kuri'a, wanda wasu suka yi fatali  da zaben saboda halin matsi na tattalin arziki da Kasar ta Iran take ciki.