1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Steinmeier ya ce a kula da juna

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 24, 2021

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bukaci al'umma da su kula da junansu yayin da ake ci gaba da fuskantar annobar coronavirus.

https://p.dw.com/p/44oBS
Deutschland Bundespräsident Steinmeier Weihnachtsgrüße
Shugaban kasar Jamus Frank-Walter SteinmeierHoto: Michael Sohn/AP Photo/picture alliance

Frank-Walter Steinmeier ya yi wannan kiranne, yayin jawabinsa na gabanin bukukuwan Kirsimetin wannan shekara. Bayan da ya yi wa al'ummar Jamus baki daya fatan alkhairi, Steinmeier ya bayyana cewa bayan kwashe kusan tsawon shekaru biyu ana fama da annobar corona, tabbas mutane na cikin kunci. Ya kara da cewa tilas a yanzu mutane su tabbatar sun dauki matakan kare kansu daga sabon nau'in na coronavirus ta hanyar yin riga-kafi, kuma yana matukar farinciki ganin mutane da dama sun fahimci cewa damar kariya tana ga allurar riga-kafin. Shugaban kasar Jamus din Frank-Walter Steinmeier ya nunar da cewa, a yanzu fiye da kowanne lokaci mutane na bukatar kulawar junansu.