Al'ummar Masar na zaben shugaban kasa
March 26, 2018Talla
Za a dauki kwanaki uku ana zaben shugaban kasar a fadin kasar ta Masar. A baya dai jami'an tsaro sun kame da dama daga cikin wadanda suka bayyana aniyar su ta takarar neman kujerar shugabancin kasar, lamarin da ya haifar da samun abokin takara daya tilo Moussa Mustafa Moussa da ya iya dagewa a kan bukatar ja da Shugaba Sisi don neman shugabancin kasar.