1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta kashe mutane 20 a Beijing

Abdul-raheem Hassan
August 1, 2023

Ambaliya ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 20, bayan saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a birnin Beijing na kasar China da lardunan da ke kewaye. Shugaban kasar X Jinping ya ware kudaden gudanar da ayyukan agaji.

https://p.dw.com/p/4Ue0z
China
Hoto: THOMAS PETER/REUTERS

Kafofin yada labaran kasar na cewa wasu mutane 19 sun bace, ana zargin watakila sun makale a laka bayan da ruwan sama ya mamaye tituna da dama tare da mamaye unguwannin da laka. Tun a ranar Juma'ar da ta gabata kudancin China ta fuskanci barazanar guguwar Doksuri bayan da ta afkawa kasar Philippines.

Shugaba Xi Jinping ya yi kira da a yi ceto sauran mutanen da laka ta binne ko ruwa ya tafi da su, tuni aka kwace sama da mutane 100,000 da ke cikin hatsari a fadin birnin Beijing. Gwamnatin Beijing ta ware kudin kasar yuwan miliyan 100 kwantankacin dalar Amirka miliyan 15 don gudanar da ayyukan agaji.