Ambaliyar ruwa a Togo
September 13, 2007Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙasar Togo, sun hallaka mutane 20, tare da jikkata wasu da dama a jihar Kpendjal, dake tazara kilomita 650, a arewancin Lome baban birnin ƙasar.
A wata sanarwa da ta hiddo, gwamnatin ƙasar ta bayana cewar gidaje dubu 22 su ka rugurguje sannan mutane kimanin dubu 40 su ka rasa matsugunai a sakamakon wannan ambaliya.
Kazalika, ruwan sun share dubbunan ekoki na gonaki, tare da kada gadoji da makarantu na karkara masu yawa.
Gwamnati ta bayyana ware kuɗi milion ɗari 5 na CFA domin kai agaji ga mutanen da ambaliyar ta rutsa da su.
Ita ma ƙasar France, ta aika jiragen sama 2, masu dura angulu, don ci gaba da ceton jama´a.
Domin nuna alhini ga wanda su ka rasa rayuka, gwamnati ta umurci yin zaman makoki na kwanaki 3 a fadin ƙasar baki ɗaya.