Ambaliyar ruwa ta yi barna a Najeriya
July 10, 2017Masu aikin ceto sun yi ta kokarin ceto jama'a a unguwar Chechenya daya daga cikin yankunan da wannan bala'i ya shafa a garin Suleja a jihar Neja da ke kuma makwabtaka da Abuja babban birnin Kasar. Ruwan sama Kamar da bakin kwarya ya yi dalilin afkuwar ambaliyar ruwan da ya haifara da wannan barna da a Hausawa kan ce ruwa ya yi gyara.
Daga cikin gidaje zuwa ga kayayyakin jama'a har ma da motoci sun zama tamkar yadda iska ke daukar leda haka ruwan sama da ya yi ambaliya ya haifar da mummunar damuwa a tsakanin al'umma, wasu yankunan garin na Suleja, baya ga gine-gine da ruwan sama ya hada rushewarsu. Malam Sulaiman Nuhu mazaunin unguwar Chechenya da ke Suleja ya bayyana irin barnar da ruwan ya yi masu. Tun kafin faduwar daminar bana, Hukumar Hasashen Yanayi ta yi gargadin cewa za'a samu ruwa mai yawa a bana da zai sauka a lokaci guda da fatan mahukunta za su dauki mataki.
Ana dai ci gaba da ambato alkaluma na yawan mutanen da suka mutu daga 11 inda wasu kafofin yada labaran ke bayyana cewa sun zarta hakan, saboda rashin samun cikakken adadi na gwamnati. Bayanai na nuna cewa fiye da shekaru 20 kenan rabon da a ga ambaliyar ruwa irin wannan a garin na Suleja da ke jihar Neja, a sauran sassan kar ma dai an sami ambaliyar ruwan a birnin Lagos al'amarin da ya kai ga tafka asarar dukiya da kuma tsayar da hada-hadar kasuwanci a jahar. A shekara ta 2012 ne Najeriya ta gamu da ambaliyar ruwa da ta fi muni a ‘yan shekaraun nan wacce ta yi dalilin mutuwar mutane 363 tare da raba wasu akalla miliyan daya da rabi da muhallansu.