Spaniya: Ambaliyar ruwa ta yi ta'adi
October 30, 2024Tuni dai gwamnatin kasar ta kafa kwamiti na musamman, domin duba irin barnar da ambaliyar ta haifar da kuma rarraba kayan agaji ga wadanda iftila'in ya afkawa. Mamakon ruwan sama da kuma kadawar iska mai karfi ta haifar da ambaliyar ruwan tun a farkon wannan makon a kudanci da kuma gabashin Spaniya, musamman a yankunan Valencia da kuma Andalusia. An samu asarar rayuka kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar, sakamakon iftila'in da ba a faye samun irinsa a kasar ba. Da dama a yankin Valencia na zaune cikin duhu kana tuni layukan waya suka daina aiki sakamakon daukewar wutar lantarki.
Firanministan kasar Pedro Sanchez ya kafa kwamiti na mussaman, domin gudanar da aikin cetoya kuma jajantawa wadanda iftila'in ya rutsa da su. A yanzu haka masu aikin ceto sun ce sun samu nasarar tseratar da mutane fiye da 200 tare da ba su mafaka a wani gidan mai, kana suna ci gaba da kutsa wa cikin yankunan domin lalubo mutanen da suka makale. Wasu mutanen dai na ci gaba da hawa kan bishiyoyi domin tsira da rayukansu, yayin da hukumomi suka shawarci mutane da su kaucewa yin tafiye-tafiye na babu gaira babu dalili saboda yadda ambaliyar ke ci gaba da mamaye hanyoyin kasar. Mutane da dama ne dai suka bayyana irin halin dimuwa da suka shiga, sakamakon iftila'in kamar yadda wasu mazauna Velancia suka bayyana.