1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amfani da soji a yaki da Ebola a Laberiya

August 7, 2014

An fara amfani da sojoji wajen tattara masu cutar Ebola a Laberiya, wannan kuwa na zuwane bayan da gwamnatin kasar ta kafa dokar tabaci a kasar.

https://p.dw.com/p/1Cr3l
Ebola in Liberia
Hoto: picture-alliance/dpa

Mahukunta a Laberiya sun fara amfani da dakarun tsaro a kokarin da suke wajen tattara rukunin jama'a da suka kamu da cutar Ebola dan kula da lafiyarsu, bayan da shubar kasar ta bayyana kafa dokar tabaci sakamakon addabar wannan cuta.

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf, tace dole al'umma su yi hakuri da irin matakan da ake dauka ganin irin mamayar rayuka da wannan cuta ke yi inda ta yi awon gaba da rayukan jama'a sama da 900 daga kasashe 4 na yammacin Afrika a wannan shekara.

Sai dai shugaban maaikatan lafiya a wannan kasa Joseph Tamba yace kafa wannan doka ya zama dole, to amma kamata ya yi a a ba wa jamaa dama su sayi kayan abinci kafin sanya wannan doka.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal