1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Amirka bayan marabus din Saad al-Hariri

Abdourahamane Hassane
October 30, 2019

Amirka ta yi kira da a gaggawata kafa sabuwar gwamnati a Libanon bayan da firaministan kasar Saad al-Hariri ya yi marabus da shi da  gwamnatinsa sakamakon matsin lamaba daga masu zanga-zanga.

https://p.dw.com/p/3SAkb
Trump verkündet Tod von IS-Anführer Al-Bagdadi
Hoto: picture-alliance/dpa/A. Harnik

A cikin wata sanarwa da sakataran harkokin wajen Amirkan Mike Pompeo ya bayyana ya bukaci 'yan siyasar na Libanon da su nuna dattako. Marabus din dai na firaminsta Libanon zai kara saka kasar cikin wani hali na rashin tabbas watanni takwas da kafa gwamnatin wacce aka kwashe dogon lokaci ana tattaunawa kafin kafuwarta.

jama'ar na  Libanon sun share kusan makonni biyu suna yin zanga- zanga domin ganin firaministan ya yi marabus, sakamakon gaza magance tarin matsalolin da kasar take fama da su na cin hanci da talauci da kuma matsalolin tattalin arziki.