1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kai wa dalibai hari a Amirka

Abdul-raheem Hassan
May 18, 2018

Hukumomin makarantar Sakadaren Santa Fe da ke jihar Texas a Amirka, sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 10 yawanci dalibai, yayin da dan bindiga ya bude wuta cikin makarantar.

https://p.dw.com/p/2xyEC
USA Texas - Schüsse auf dem Kampus der Santa Fe Schule
Hoto: Reuters/Courtesy HSCO

Babu cikakkun bayanai kan maharin kawo yanzu, sai dai jami'an tsaro na tsare da wani tsohon dalibin makarantar da ake zargi. Hukumomin makarantar na dangata harin da ta'addanci.

Wannan hari shi ne na baya-bayannan tun bayan wani mumunan harin da ya halaka dalibai 17, a wata makarantar sakadare a jihar Florida. Abinda ya haifar da zanga-zangar dalibai kan neman hukumomi su tsaurara dokar mallakar bindiga a Amirka.

Mataimakin shugaban Amirka Mike Pence, ya bayyana kaduwar gwamnati kan lamarin. Yace: "Shugaban Donald Trump ya nuna jimamin aika-aikan da yafaru kan dalibai, kuma za mu ci gaba da bin diddigin al'amarin. Gwamnati a shirye take ta ba da duk guddumuwa ga wadan da harin ya shafa."