1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Chaina za su yi aiki tare

Ramatu Garba Baba
November 11, 2021

Amirka da Chaina da suka fi kowacce kasa fitar da hayakin da ke gurbata yanayi sun dauki alkwarin yin aiki tare a daukar matakan da suka dace kan dumamar yanayi.

https://p.dw.com/p/42qqw
G20 Rom | Antony Blinken trifft Wang Yi
Hoto: Tiziana Fabi/pool/AP/picture alliance

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga kwanakin karshe na taron koli da ke gudana a birnin Glasgow. Kasashen Amirka da Chaina da su suka fi fitar da hayakin da ke gurbata yanayi a duniya sun amince tare da daukar alkwarin daukar matakin ceto duniya daga halin da take ci a sakamakon ayyukan dan adam, da ke haifar da matsalolin da dumamar yanayi ke janyowa.

Wannan na nufin kasashen biyu sun amince da kiran da aka jima ana yi na daukar matakin gaggawa da ke bukatar hadin kai a shawo kan matsalar sauyin yanayin. Sanarwar ta ba-zata ta zo cike da mamaki saboda takardamar da ke a tsakanin kasashen biyu kan batutuwa da dama, ciki kuwa har da wannan batu na sauyin yanayi. Chaina da Amirka ke fitar da kashi akalla arba'in cikin dari na hayaki da ke dumama yanayi a duniya.