Amirka na kan gaba wajen cinkin makama a duniya
December 7, 2020Wani rahoto da wata cibiyar bincike kan zaman lafiya ta SIPRI ta fitar na nuni da cewa kasashen Amirka da Sin ko China sune kan gaba wajen cinikin makamai a fadin duniya.
Haka zalika, a karon farko kasashen yankin gabas ta tsakiya sun shiga sahun kasashe 25 da ake kera makamai. Rahoton ya ce kasashe kalkashin kungiyar EU ka iya kamo Amirkar da China idan aka jimlacesu.
Kasar Amirka na kan gaba da kashi 61 cikin dari inda ta doke China da kashi 15.7 na makaman da ake sayarwa, wanda jimillar kudadensu ya kai dalar Amirkar miliyan dubu dari uku da sittin da daya. kiyasin hakan ya linka abinda Majalisar Dinkin Duniya ke kashewa har sau 50 wajen kokarin samar da zaman lafiya a duniya.
Kimanin kamfanonin Amirka shida ne da kuma na China uku ke wannan harkar.