Rikicin Amirka da Iran na kara zafi
September 17, 2019Tuni dai kungiyar 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka dauki alhakin kaiwa wadannan hare-haren, sai dai Amirka da Saudiyya na zargin Iran da kai hare-hare, zargin da mahukuntan Tehran din suka musanta.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan wani taro da ya gudanar a Litinin din da ta gabata da mukarrabansa inda suka yi nazarin halin da ake ciki da kuma matakan dauka, Shugaba Donald Trump na Amirka ya bayyana hare-haren da aka kai Saudiyyan a matsayin gagarimin harin da ya kamata kasarsa ta mayar da martani mai karfi.
Sai dai babban sakataren kungiyar kare hakkin dan Adam ta kasa da kasa Amnesty International Kumi Naidoo ya yi gargadin cewa duk wani matakin soja da Amirka za ta dauka kan Iran, zai kara dagula al'amura ne kawai a yankin Gabas ta Tsakiya.