1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka da Rasha na duba makomar Siriya

Yusuf BalaMay 3, 2016

Bayan kwararar da jinin a birnin Aleppo, rikicin dai 'yan makonni da suka bata ya yi sanadi na rayukan mutane 250.

https://p.dw.com/p/1IgrQ
John Kerry Staffan de Mistura Genf Schweiz
John Kerry da Staffan de Mistura a lokacin taron manema labaraiHoto: Reuters/D.Balibouse

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya bayyana cewar mahukuntan birnin Washington da Rasha sun amince da aiki tare dan tabbatar da ganin lugudan wutar da ake a Arewacin Siriya ya takaita. Mista Kerry ya gana da jakadan Majalisar Dinkin Duniya Staffan de Mistura a birnin Geneva bayan fiye da mako guda da aka yi ana kwararar da jinin a birnin Aleppo, rikicin da ya yi sanadi na rayukan mutane 250.

Shi kuwa Philip Hammond, sakatren harkokin wajen Birtaniya cewa ya yi akwai bukatar ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarori da ke gaba da juna a kasar ta Siriya:

"A kwai bukatar samar da sabbin tsare-tsare da ganin an ci gaba da tattaunawar da ake tsakanin masu gaba da juna, abu ne da ke da wahala masu sassaucin ra'ayi da ke shiga wannan tattaunawa daga Siriya su ci gaba da zama yayin da ake ci gaba da kashe al'ummarsu."

A wani bayani da ke fita daga fadar ta Kremlin dukkanin su biyun Rasha da Amirka sun amince da wasu matakai da za a dauka sai dai babu karin bayani kan wadanne matakai ne.