1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka: Kalubale kan yarjejeniyar nukiliyar Iran

Salissou Boukari
October 14, 2017

Kasashen da suka rattaba hannu a yarjejeniyar kasa da kasa kan batun nukiliyar Iran, sun sanar da damuwarsu bayan da shugaban Amirka ya dauki matakin da ka iya sa ya fice daga yarjejeniyar a kowa ne lokaci.

https://p.dw.com/p/2lp6S
USA Trump
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Reuters/K. Lamarque

Cikin jawabin da ya yi, Donald Trump ya caccaki kasar Iran inda ya danganta ta a matsayin wadda ta ke daurewa ta'addancin gindi, sannan ya ce bai gamsu da yarjejeniyar ba:

"Dole ne mu kira ciwo da sunansa, muna goyon bayan abokanmu da sauran abokan tafiyarmu, zamu kulla sabuwar hullar dangantaka ta zaman lafiya, don haka dole mu dauki matakai kan wadanda ke zama barazana ga al'ummarmu."

Wadannan kalamai na shugaban Amirka na zuwa ne duk da tabbacin da hukumar kasa da kasa mai kula da makamashin nukiliya ta IAEA ta bayar na cewa kasar Iran na bin dukannin matakan da aka gindaya mata fiye da duk wata kasa. Sai dai da yake magana kan wannan mataki shugaban kasar Iran Hassan Rohani cewa ya yi, idan har hakarsu bata cimma ruwa ba, to dole su dauki mataki:

" Zamu ci gaba da hulda tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa bisa ga tsari, kuma daidai da yarjejeniyar da aka cimma. Amma kuma idan cikin tafiyar muka ga cewa muradunmu ba su cika, ko kuma wani bangare bai cika nashi alkawari ba, to ba zamu yi wata-wata ba wajen daukar mataki."

Cikin wata sanarwa da kakkausar murya, Firaministar Britaniya Theresa May, da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel, da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, sun sanar cewa za su ci gaba da kasancewa cikin wannan yarjejeniya da aka cimma da Iran, tare da yin kira ga kowane bangare da ya yi biyayya wajen tafiyar da ita.