Amirka: Kotun Brooklyn ta hana korar wasu baki daga kasar
January 29, 2017Talla
Kungiyoyin kare hakin bil-Adama na kasar ne dai suka shigar da kara na gaggawa a gaban alkalin Brooklyn, wadda ta bada umarni ga hukumomin kasar da kadda su aiwatar da korar mutun ko daya. Lauyan da ke kare kungiyoyin Lee Gelernt ya sanar wa masu zanga-zanga cewa:
" Alkallan kasar Amirka ba za su bada izinin korar kowa daga cikin wadanda yanzu haka suke tsare a filayen jiragen sama ba. sannan kuma alkalin ta ce a kawo mata dukannin sunayen mutanen da ake tsare da su a filayen jiragen, da kuma ake shirin kora a karkashin wannan kudiri na Shugaba Trump."
Wannan batu na korar ya shafi 'yan kasashen Iran, Iraki, Yemen, Somaliya, Libiya, Siriya da kuma Sudan, wadanda suke da takardun izinin shiga kasar ta Amirka.